Shugaban Kasa

0
1816

>Rabo Haladu, daga kaduna

AN bayyana matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake dauka na farfado
da ci gaban tattalin arzikin kasa a matsayin  abin jinjina ga shugaban
kasa.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar masu canji na jihar,
Alhaji Dallatu Haruna Jumare, inda ya ce kungiyarsu tana goyon bayan irin
matakan da shugaban Muhammadu Buhari yake dauka na kawo ci gaban tattalin
arzikin kasar nan baki daya.
Shugaban ya bayyana haka ne jim kadan bayan wata kungiyar \’yan jarida mai
suna Kaduna Media Forum suka karrama shi da lambar yabo.
A nasa jawabin shugaban kungiyar, Alhaji Muhammadu usman, ya yaba da irin
gudummawar da kafafen yada labarai suke takawa na tallafa wa gwamnati
tarayya wajen fadakar da su dangane da irin manufofin gwamnati baki daya .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here