‘Yan Kwallon Najeriya U17 Sun Kacaccala Takwararsu Na Burazil Da Ci 3-0

0
1107

 

Daga Wakilinmu

‘YAN wasan kwallon kafa na U17 masu buga wa kasar Najeriya sun yi rawar gani a wasansu da kasar Burazil inda suka lallasa Burazil din da ci uku da nema tun a farkon rabin lokaci inda nasarar cin kwallayen ta zo kusan kamar mafarki ga ‘yan kwallon Burazil din, domin kwallayen guda uku a ragar tasu sun zo ne duka a cikin mintina uku zuwa biyar a takaitawa.

Wasan dai ya kayatar domin an nuna gwaninta da kwarewa na murza kwallon kafa, domin dai duniya ta san kasar ta Burazil din da iya murza leda, sai dai kawai sa’a na kan ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya.

Da nake zantawa da wani mai sha’awar kwallon kafa kuma magoyin bayan Burazil, Barisa Abdullahi Maikano, ya ce, ko shakka babu Najeriya tana murnar kokarin da ‘yan wasan nasu suka yi, amma kwallon ta nuna kasar Burazil.

Baristan ya kuma ce, ai ko babu komai su ‘yan U17 na Najeriya, suna kokarin nuna kansu ne, kuma sun nuna, abin da ake jira kawai,su yi kokarin kawo wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari kofin nan, don kuwa a yanzu gwamnatin canji ce a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here