Lambar BVN Yaushe Za A Kammala Aikin?

  0
  2402

  Isah Ahmed Daga Jos Da Imrana Abdullahi Daga kaduna

  A bisa dukkan alamu da mutum zai iya gani da idanunsa batun lambar tsaron da bankuna ke kokarin yi domin samar da ingantaccen tsaron dukiyar jama\’a musamman masu ajiyar kudi a bankuna,aikin na neman kai kasu yinsa tamkar aikin wankin hula ne da ke neman kai jama\’a dare.

  Wannan lamari ya fito fili ne tun bayan da lokacin da aka dibar wa aikin ya kare amma kuma ba a kammalawa jama\’ar da ke ajiyar kudinsu a bankuna ba wannan lamba.

  Rahotannin da suka fito fili na nuni da cewa har yanzu ba a kammala yin wannan lamba ba ga rabin masu yin ajiyar kudinsu a banki,kamar yadda rahotannin suke nuna wa cewa da akwai mutane masu yin ajiyar kudinsu a banki mutane miliyan 50 amma ya zuwa yanzu babban bankin Najeriya ya tabbatar da cewa an yi wa mutane miliyan sama da Ashirin ne wannan lambar saboda haka ne jama\’a da dama ke cewa shin wai a yaushe ne za a kammala aikin tun da lokacin da aka dibar wa aikin yazo karshe?

  Shugaban kungiyar masu sayar da buhuna ta jihar Filato Alhaji Iliyasu Muhammad, ya bayyana cewa lambar tantancewa da bankunan kasar nan suke baiwa masu ajiya a bankunan, wata babbar kariya ce ga masu ajiyar.
  Alhaji Iliyasu Muhammad ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu kan cikar wa\’adin bayar da wannan lamba da bankuna  suka yi a makon da ya gabata.

  Ya ce  tsarin lambar tantancewa ta BVN da bankuna suka baiwa masu ajiya dasu, abu ne wanda yake da matukar amfani a wajen bankuna da masu hulda dasu da kuma  gwamnati.

  \’\’Domin kai mai ajiya a banki wannan tsari zai tsare maka dukiyarka wajen magance  miyagun da  suke cirewa mutane kudadensu a bankuna.
  Kuma  tsari zai baiwa gwamnati dama ta rika ganin dukkan abubuwan da ke faruwa a asusun  masu ajiya a bankuna.

  Don haka ya yi kira ga bankuna kasar nan, kan su kara lokaci don sauran masu ajiya da ba su karba ba  wannan Lamba ta tantancewa ta BVN ba, su samu su karba.

  Har\’ila yau ya yi kira ga jama\’a masu ajiya a bankunan kasar nan da ba su sami karbar wannan Lambar tantancewa ba,    su hanzarta zuwa su karbar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here