Daga Mohammad Ibrahim, Kaduna
Shahararren dan jaridan nan da ya yi suna a Najeriya da nahiyar afrika baki daya mazaunin jahar Kaduna Malam Abdulkareen Albashir, ya samu taimakon kafar roba daga Senata Shehu Sani, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta kasa.
Malam Albashir, dai ya rasa kafarsa daya ne a sakamokon wata rashin lafiya da ya yi shekara daya kenan da rabi.
Sanata Shehu Sani da yake jawabi a lokacin da yakai wani kwararren likita gidan dan jaridar da ke a unguwar kinkinau a cikin garin kaduna domin ya auna kafar da za\’a yi masa, ya ce Malam Albashir dan jarida ne da ya taimaka wajen ci gaban kasar nan.
\” Yau shekara daya da rabi kenan da ya rasa kafarsa daya amma babu wani taimako da aka kai masa musamman wajen gyara masa kafa. Wannan ne yasa muka ga ya dace mutaimaka masa da kafar roba da za ta taimaka masa wajen gudanar da aiyukansa na yau da kullum.
\” Abin bakin ciki ne yadda shugabanin da suka jagoranci kasar nan ba su san taimakawa marasa galihu bayan Allah ya wadata kasar nan da dukiya mai yawan gaske. Malam Albashir kuwa mutum ne da ya bada gudunmuwarsa wajen ci gaban kasar nan ta hanyar rubuce-rubucensa,\” inji shi.
Senata Shehu Sani ya ce wannan kafar roba da za\’a yi masa zai ci kudi dalar Amurka dubu uku kusan naira Dubu dari biyar kenan kudin Najariya.
Shi kuwa da yake mayar da jawabinsa, Malam Abdulkareem Albashir, godiya ya yi ga Sanata da ya kawo masa dauki.
Ya ce hakika akwai mutane daban -daban da ke kawo masa taimako wanda kuma hakan yasa yake mika godiyarsa ga duk masu taimaka masa.
A cewarsa, ya yi imanin cewa alherin da ya aikata ne ta sanadiyar aikinsa yasa mutane ke tunawa da shi har suke kawo masa taimako.