An Nemi Gwamnatin Gwamna El-Rufa’I Da Ta Agaji Firamaren Rigasa

0
1520

Usman Nasidi Daga Kaduna

A sakamakon shirin bayar da  ilimi kyauta da gwamnatin Jihar Kaduna ke yi, akalla sama da yara dubu 30 ne aka dauka a makarantar firamaren da ke titin Lakoja, Rigasa Kaduna.

Wani jami\’in hukumar makarantar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa duk da yawan yaran da suke fama da shi, har yanzu ba su daina daukar yaran ba, don gwamnatin Jahar ba ta umarce su da daina yin hakan ba.

Majiyar, ta kara da cewa a bisa kiyasin da suke da shi na sababbin yaran da aka dauka kuma aka yi musu rajista a yanzu suna da sama da dubu 30, ban da kuma yaran da ba a kai ga yi masu rajista ba, da kuma yaran da dama suke da su a da a makarantar.

\” Mafi akasarin yaran na karatu ne a tsakiyar filin harabar makarantar domin babu azuzuwan da za mu saka yaran a yanzu, sai dai nan gaba kila idan gwamnatin jihar ta gina musu wasu azuzuwan.\”

A cewarsa, yaran na fama da matsalar ruwan da za su sha ko yin amfani da shi wajen wata lalurar, duk da yake kantomar karamar hukumar, Malam Yusha\’u Ibrahim a wata ziyarar da ya kai makarantar, ya yi masu  alkawarin taimakawa da rijiyar burtsatse, ganin irin yadda suke cikin wani mawuyacin hali.

Majiyar, ta kuma kara da cewa ya yi masu alkawarin gina bayin zagayawa bayan gida da fitsari, wanda za a rika kula da shi don guje wa kamuwa da duk wata cuta a sakamakon ganin irin cudanyar da yaran ke yi a wuraren da suke amfani da shi a yanzu.

A karshe, majiyar ta bukaci gwamnatin jihar da duk wasu masu hannu da shuni musamman iyayen yara, da su kawo musu agaji na gaggawa don ganin an magance wannan matsalar da suke fama da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here