Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNATIN Jihar Kano ta kafa wani kwamiti domin binciken zarge-zargen da ake ta samu daga jama’a da yawan gaske na cewa, ana yi wa yara dalibai fyade a makarantar Hassan Gwarzo.
Farfesa Abubakar Mustapha, tsohon shugaban Jami\’ar Maiduguri shi ne zai jagoranci kwamiti mai wakilci daga ma\’aikatan gwamnati da masarauta da jami\’an tsaron da lauyoyi da kuma kungiyoyin kare hakkin bil\’adama. An bai wa kwamitin makonni biyu domin ya mika sakamakon bincikensa.
Abubuwan da kwamiti zai yi sun hada da binciken gaskiyar al\’amari da wadanda aka yi wa fyaden da wadanda suka yi da kuma ko makaranta tana da hannu a ciki ko babu.Wannan dai yana zuwa ne \’yan sa\’o\’i bayan da gwamnatin Jihar ta bayar da umurnin rufe makarantu.
A ranar Alhamis ne wasu dalibain makarantar da iyayansu suka yi zargin cewa wasu daliban na yi wa yaran fyade ko kuma a wasu lokutan yunkurin yi musu fyade.
A ranar Alhamis ne wasu dalibain makarantar da iyayansu suka yi zargin cewa wasu daliban na yi wa yaran fyade ko kuma a wasu lokutan yunkurin yi musu fyade.