Hukumar SEMA A Jihar Filato Ta Kai Wa \’Yan Gudun Hijira Dauki

1
1417

Isah Ahmed, Daga Jos

HUKUMAR agajin gaggawa ta Jihar Filato [SEMA] ta kai wa \’yan gudun hijirar rikicin  da aka yi a wasu yankuna na kananan hukumomin Barikin Ladi da Mangu da ke jihar tallafin kayayyakin abinci da na gini.


Kayayyakin da hukumar ta kai sun hada da buhunan  masara da shinkafa da wake da manja da gishiri da barguna da tabarmai da katifu da gidajen sauro da kwanon rufi da buhunan siminti da kusoshi.

Da yake mika kayayyakin agajin ga shugaban riko na karamar hukumar Barikin Ladi, Mista Bitrus Doro, sakataren hukumar agajin gaggawa ta Jihar Filato [SEMA] Alhaji Alhassan Barde ya bayyana cewa  mai girma gwamnan jihar Filato, Barista Simon Lalong ne ya ba da kudaden da aka sayo wadannan kayayyaki don a raba wa wadanda wannan rikici ya shafa,
don nuna tausayawa a gare su.Ya ce kudaden  da aka kasha sun kai naira Miliyan hamsin da biyar.

Ya yi kira ga jami\’an kananan hukumomi na  Barikin Ladi da Mangu su tabbatar da cewa kayayyakin  sun isa hannun wadanda aka yi domin su.

Har ila yau ya yi kira ga al\’ummomin yankunan da wannan rikici ya shafa, su sasanta junansu su zauna lafiya domin a sami kwanciyar hankali da ci gaba a yankunan.

Da yake karbar kayayyakin tallafin shugaban riko na karamar hukumar Barikin Ladi, Mista Bitrus Doro ya bayyana matukar farin cikinsu ga wannan tallafi da aka kawo masu.

Ya ce tuni sun kafa wani  kwamiti a wannan karamar hukuma wanda zai aikin ganin  wadannan kayayyaki sun isa ga wadanda wannan rikici ya shafa.

Daga nan ya nuna takaicinsa  kan  irin wadannan rikicerikice da suke faruwa a  karamar hukuma ta Barikin Ladi.

\’\’Abin da takaici ganin yadda mutanen da suka yi shekara da shekaru suna zaune lafiya da junansu amma yanzu sun zo suna irin wannan fadace- fadace da junansu. Ya kamata mu  guji irin wadannan rikicerikice mu zauna lafiya da junanmu domin samun kwanciyar hankali da ci gaba\’\’

1 COMMENT

  1. LALLAI wannan agaji ya yi kyau saboda mutane da yawa sun shiga cikin wani halin kakanikayi amma da wannan kokari za a taimaki mutane da yawa su dawo cikin hayyacinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here