Filin RAHA: ASSIKI MUNA SO

0
4132
Daga Zubairu A. Sada
WANI Bayarabe ne da ke zaune tare da abokan wasansa Sakkwatawa. Sai wata rana ya nemi da a ba shi ‘wurudi’ domin ya nemi na jari, wani cikinsu ya hada shi da malami wanda ya sanar da shi wuridin da zai yi, ya ce masa za ta yiwu wani ‘Aljani’ ya zo wurinsa ya tambaye shi abin da yake so, sai ya fada mashi. Hakan kuwa aka yi, wata rana da tsakar dare sai ya ji an tambaye shi, mene ne kake so ne kake damunmu? Sai gogan naka ya furta cewa, ‘’assiki muna so kawai’’. Yana nufin ‘arziki.  Shi kuwa aljani ya ji kamar an ce aski, sai ya shafa wa Bayarabe kai, take gashinsa na kai ya zube. Ya yi ihu ya ce, ‘’assiki ba asuki ba fa’’, ina! Aljani tuni ya bace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here