Sana\’ar Gyaran Takalma Ta Yi Mani Komai—Aminu Mai gyaran takalma

    0
    2535

    Isah Ahmed, Daga Jos

    AMINU Muhammad Saminka mai sana\’ar gyaran  takalma a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, matashi ne da ya yi fice kan sana\’arsa ta hada takalma tare da gyaran takalman a yankin na Saminaka da kewaye. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana cewa  wannan sana\’a ta yi masa komai. Don haka ya shawarci matasa kan su rungumi sana\’a don kare mutuncinsu.

    Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
    GTK: A wanne lokaci ne ka fara wannan sana\’a ta gyaran takalma?
    Aminu: Na fara koyon wannan sana\’a ta gyaran takalma  ne tun a shekara ta 2003 a wajen maigidana a nan garin
    Saminaka. Na yi aiki da wannan maigida nawa har na tsawon shekara 5 da wasu watanni. Bayan haka ya yaye ni a shekara ta 2009,  daga nan nazo na bude wannan shago nawa a shekara ta 2010.
    GTK: Yaya kake yi wajen gudanar da wannan sana\’a?
    Aminu: To yadda nake gudanar da wannan sana\’a shi ne nakan tashi daga nan, na je Jos ko Kano na sayo kayayyakin hada takalman nan, na zo na hada na  sayar da kwaya daya-daya wani lokaci ma har nakan bayar da sari.

    GTK: Mene ne ya Karfafa maka gwiwar rungumar wannan sana\’a?
    Aminu: Babban abin da ya Karfafa mani gwiwar  shiga wannan sana\’a shi ne yanayi irin na rayuwa. Domin rayuwa a yau ko da mahaifinka  wani babba ne ko kuma kana ganin kai wani ne, yana da kyau ka kama wata sana\’a, domin ko da ka yi karatu, idan ba ka sami aiki ba, za ka iya yin wannan sana\’a domin ka rufa wa kanka da iyayenka asiri. Shi ne abin da ya Karfafa mani gwiwar rungumar wannan sana\’a.

    GTK: Daga lokacin da ka fara wannan sana\’a zuwa yanzu wadanne irin nasarori kake ganin ka samu?

    Aminu: A gaskiya na sami nasarori da dama a wannan sana\’a domin na yi aure da wannan sana\’a na sami jari na sayi mashin din hawa na biya wa kaina kudin makaranta da \’yan uwana duk da wannan sana\’a, kuma ina da yara guda hudu da suke karkashina a wajen wannan sana\’a.

     GTK: Mene ne babban burinka kan wannan sana\’a?
    Aminu: Babban burina kan wannan sana\’a shi ne na kasance na ingantata, ya zamanto ina yin takalma masu rufi. Bayan haka a yanzu haka na cika fom na makarantar koyon sana\’ar hada takalma da jakankuna da huluna da ke Zariya, domin na je na koyo tsari irin na zamani domin na zo na dada bunkasa wannan sana\’a.

    GTK: Mene ne babbancin irin takalman da kuke hadawa da irin takalman da ake shigowa da su daga waje?

    Aminu: Takalman da ake shigowa da su daga waje suna dauke da ranar mutuwarsu,kuma za ka samu sukan yi saman da kyau amma kasan babu kyau. Mu kuma namu mukan sayo kayan ne mu hada shi gwargwadon amincinsa gwargwadon kudinsa.
    GTK: Wane irin tasiri ne kake ganin wannan sana\’a take da shi wajen samar da ayyukan yi ga matasa?
    Aminu: Babu shakka wannan sana\’a tana da tasiri wajen samar da ayyukan yi, domin tana hana zaman banza  kuma  matasa suna samun kaya a farashi mai sauki a wannan sana\’a.

    GTK: Wane kira kake da shi zuwa ga gwamnati dangane da muhimmancin tallafa wa irin wadannan kananan sana\’o\’i?

    Aminu: Kiran da zan yi wa gwamnati shi ne a duk lokacin da aka ga wani abu musamman irin wadannan kananan sana\’o\’i a tallafa masu, domin akwai jama\’a da dama wadanda sun iya irin wadannan sana\’o\’i amma saboda rashin jari sun kasa aiwatar da su. Don haka ina
    kira ga gwamnati kan ta rika bai wa masu kananan sana\’o\’i rancen jari domin su yi wannan sana\’a su debi yara aiki, sai a rage wa gwamnatin rashin aikin yin a matasa.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here