An Bukaci Fani Kayode Ya Nemi Gafarar Fulani

0
1405
HADADDIYAR kungiyar al\’ummar Fulani ta kasa mai suna Miyatti Allah Kautal Hore ta aika wa tsohon ministan kasar nan,  Femi Fani -Kayode da sakon gargadi bisa cin fuskar da suka ce ya yi wa al\’ummar Fulani.
Sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Bello Abdullahi Bodejo ne ya bayyana hakan bayan kammala taron da suka yi da shugabannin kungiyar na shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya a Abuja.
Kamar yadda Bodejo,ya bayyana cewa shi Fani-Kayode ya taba kiran Fulani da kudan tsando, ya kuma ce a tashi duk Fulani daga kudancin Najeriya wanda haka ba daidai ba ne ya aiwatar da irin wannan furuci.
Shugabannin sun yi kira ga fani-Kayode da cewa, idan har bai nemi gafara daga gare su ba to lamarin zai tilasta masu zuwa kotu domin neman hakkinsu,\”Muna son shi Fani Kayode ya fito fili ya nemi gafara a kan kalamansa da ya yi wanda a fili suna nuni ne da cewa ya tsane mu, don haka idan bai yi kokarin neman afuwa ba, to, shari\’a za ta raba mu\”

Bodejo,ya kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari,da ya tabbatar ana sa idanu a kan irin wadannan kalamai na nuna tsana ga wata al\’umma domin a samu cikakken hadin kai a tsakanin jama\’ar kasa baki daya.
\”Muna son gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar ta hukunta duk wani mutumin da yake yin kalamai irin wadannan ko mai girman mukaminsa\”
IMRANA ABDULLAHI DAGA KADUNA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here