Saraki Ya Bayyana A Kotu

  0
  1351

  BAYANAN da muka samu a halin yanzu na tabbatar mana da cewa shugaban majalisar Dattawan Najeriya Sanata Abubakar Olu Sola Saraki ya isa kotun da ke yi masa shari\’a a game da batun karyar daake zargin ya yi kan bayyana kadarar da ya mallaka.
  Ya dai isa wannan kotun ce da ke aiki a game da duk wani mutum da ya samu matsala a kan bayanin da ya bayyana mata domin kyaran akida ta yadda za a daina samun ma\’aikatan da za su kasa tabbatar da bayanin kaddarorin da suka mallaka a lokacin da za su dare kan karagar mulki ko wani aiki a fadin kasa baki daya.

  Majiyarmu ta bayyana mana cewa ya isa kotun ne da tawagar sanatoci a kalla 35 kuma suna zaune a kan wuraren zaman kotu guda shidda da dama aka yi tanadi.
  Idan dai masu karatu za su iya tunawa a lokacin da Saraki ya halarci kotun a ranar 21 ga watan Okutoba ya samu rakiyar sanatoci 81 ne a tare da shi.
  Kadan daga cikinsu sun hadar da sanata Ike Ekweremadu,wanda shi ne mataimakinsa dan (PDP) sai Sam Anyanwu (PDP),Andy Uba (PDP),Adamu Aliero (APC),Shehu Sani (APC),Dino Melaye (APC), Tayo Alasoadura (APC),Kabiru Gaya (APC) da kuma Uche Ekwunife (PDP).

  Saraki dai ya fara halartar kotun ne a ranar 22 ga watan satumbar da ya gabata bayan da kotun ta bayar da kotun kula da bayanin kaddarorin ma\’aikatan ta bayar da  odar a kama shi.

  Ya kuma bayyana wa kotun cewa shi bai yi wani laifi ba a laifuka 13 da kotun ke tuhumarsa a kai tun bayan da aka ce ya kasa yin bayanin kaddarorin da ya mallaka duk da cewa ya zama shugaban majalisar Dattawan najeriya.

  Duk da yake ya halarci kotun da kansa amma duk yunkurin da ya yi na hana ci gaban shari\’ar a babbar kotun tarayya lamarin ya ci tura.
  Koda yake dai ya tafi kotun karshe da ake kira kotun Allah ya isa domin a ajiye batun a gefe amma ana jiran kotun ta fara sauraren karar.
  Wannan shi ne karo na uku da yake halartar kotun domin ya bayyana a kotun a karo na biyu  ne a ranar 21ga watan Okutoba inda aka dade shari\’ar bisa zargin cewa yana da kara a kotun daukaka kara ta kasa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here