Wani Dan Sanda A Kaduna Ya Kashe Tsohuwar Matarsa

0
2234


Usman Nasidi
, Daga Kaduna

WANI kofur na ‘yan sanda, Abdulaziz  Ali, da ke aiki a barikin jami\’an tsaro na Mopol a Kaduna, ya kashe tsohuwar matarsa a yayin da ta je kwashe kayanta a gidansa da ke barikin bayan mutuwar aurensu.

Wata majiya kuma makwabtansu da ke zaune a yankin Garejin Television, ta bayyana cewa Safiya ta je kwashe kayanta ne tare da wasu mutane biyar, amma sai da ta fara zuwa wajen wani (Provost) mai gidan mijin nata a nan barikin don ta sanar da shi.

Majiyar ta kara da cewa ganin hakan ya sanya mai gidan ya aika aka kira mijin nata, kuma ya amsa kiran ba tare da wata jayayya ba, kana aka hada su da wasu jami\’an ‘yan sanda guda biyu don su je gidan su ga ta kwashe kayanta cikin kwanciyar hankali.

A cewar wata majiyar da take ganau ba jiyau ba, daya daga cikin ‘yan sandan na dauke da bindiga, a yayin da dayan ba ya rike da komai  kuma shi mijin nata yana ta kokarin taimaka musu wajen kwashe kayan, ya boye manufarsa kuma yana da wata bindiga a dakinsa .

Hakazalika, kafintan da ta zo da shi don ya taimaka mata wajen cire gadonta, ya bayyana cewa yana cikin aikin sai Kofur Ali ya shigo ya ce mishi zai dauki wani abu a karkakashin gadon, amma kafin ya farga, sai ya ji karar bindiga da kuma na Safiya da take cikin kichin din da ke kusa da dakin. Ya ce \”bayan harbin da Kofur Ali ya yi, sai ya fita waje yana ihun ya kashe maman Zainab kafin ya jefar da bindigar, ya ketare katangar barikin inda ya mika kansa  a ofishin bincike na C.I.D da ke jihar.\”

Safiya da Abdulaziz dai na da wata yarinya ‘yar kimanin shekara uku kafin mutuwar aurensu , don bayan rabuwarsu ma har ta koma gidansu a Jihar Adamawa kafin ta sake dawowa domin kwashe kayanta a inda ta gamu da ajalinta.

Kawo yanzu da muka kawo muku wannan labarin, wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin jami\’in hulda da jama\’a na rundunar  ‘yan sandan Jihar Kaduna, DSP Zubairu Abubakar kan wannan  lamari, amma abin ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here