Rabo Haladu Daga Kaduna
BABBAN sifeton \’yan sandan Nijeriya, Solomon Arase, ya gargadi mutanen da ke shirin yin zanga-zanga domin neman ballewa daga kasar Najeriya don kafa kasar Biafra da su kuka da kansu, kuma su sani cewa, Najeriya ta fi karfin wani bangare guda ya kawo mata rashin zaman lafiya da zaman tare a matsayin kasa daya dunkulalliya.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar,wacce mai Magana da yawun rundunar, Olabisi kolawole ya sanyawa hannu ta ambaci Babban sifeton ‘yan sandan na cewa.
\”mun samu labarin da ke cewa wasu za su yi zanga-zanga da muggan makamai a sassa daban-daban na yankin kudu maso gabas hakan wani yunkuri ne na tayar da zaune-tsaye, don haka muna so a sani cewa dokar hana mallakar makamai ba bisa ka\’ida ba na nan tana ci gaba da aiki.
Rundunar ta ce duk wanda ya nemi kawo hatsaniya kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba zai fuskanci fushinta.
Sai rundunar ‘yan sandan ta bukaci mazauna yankin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, tana mai cewa za ta kare su daga duk wata barazana da ka iya tasowa.
A jiya ne dai magoya bayan ballewa daga Najeriya su sami kasar Biafara din suka fito kwansu da kwarkwatarsu suna yin za