Daliban Jihar Gombe Sun koka Da Mawuyacin Hali

0
1425
RABO HALADU, Daga Kaduna
 DALIBAN makarantar koyan aikin  lauya ta Nijeriya \’yan asalin jihar Gombe sun koka da abin da suka kira mawuyacin hali da suke ciki, sanadiyyar rashin ba su kudin tallafin karatu da gwamnatin jihar ta saba bayarwa.

Daliban sun ce wasun su sun ci bashin kudin fiye da Naira dubu dari uku kowannensu, domin su biya kudin makaranta da kuma wasu hidindimun karatun, amma har kawo yanzu gwamnatin ba ta waiwaye su ba. Daliban sun bukaci gwamnatin ta kawo masu dauki.

A duk shekara dai gwamnatoci da dama kan bai wa dalibain jihohinsu tallafin karatu a makarantar aikin lauya saboda tsadar da karatu a makarantar ke da shi.

Jami \’an gwamnatin dai sun ce za su gudanar da bincike a kan zargin da daliban suke yi, su gano gaskiyar lamarin na an biya su koko ba a biya su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here