Mun Gina Masallacin Juma\’a Domin Mu Bayar Da Gudunmawarmu – Sheikh Jingir

0
3219
Isah Ahmed Daga Jos

Shugaban majalisar malamai na Kungiyar Jama\’atu Izalatil Bid\’ah Wa\’ikamatis Sunnah ta Kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya bayyana cewa  kungiyar tana gina babban  masallacin Juma\’a a babban birnin tarayya Abuja ne, don bada gudunmawarta wajen raya birnin.

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara wajen da ake gudanar da wannan aiki a Abuja a karshen makon da ya gabata.

Ya ce mun yi sama da shekara  10 muna fadi tashin wannan aiki na gina masallacin Juma\’a a Abuja, ganin mahimmancin wannan aiki ya sanya muka kafa kakkarfan kwamitin gudanar da aikin karkashin jagoranci tsohon ministan Abuja Dakta Aliyu Mudibbo.

Sheikh Jingir, ya nuna gamsuwarsa kan yadda aikin gina wannan masallaci yake tafiya, don haka ya yabawa \’yan kwamitin aikin  da injiniyoyin da suke gudanar da aikin.

Ya ce ya zuwa yanzu mun sami gudunmawar miliyoyin kudade  don gudanar da wannan aiki, kuma zamu amfani da wadannan kudade wajen gudanar da wannan aiki.

Ya kuma yi kira ga jama\’a kan a cigaba da taimakawa wannan babban aiki da kungiyar ta sanya a gaba.

Daga nan ya gargadi jama\’a kan  su lura kada su bari wasu suyi amfani da wannan masallaci wajen neman gudunmawa don su cuce su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here