An Rufe Gidajen Mai 23 A Filato

  0
  1949

  Isah Ahmed, Daga Jos

  HUKUMAR kula da albarkatun man fetur ta kasa ta rufe gidajen mai guda 23 a Jihar Filato saboda an same su da laifin sayar da man fetur sama da farashin gwamnati, a karshen makon da ya gabata.
  Babban jami\’in hukumar da ya jagoranci gudanar da wannan aiki, Cif 
  Caesar Douglas ne ya bayyana haka, a lokacin da yake zantawa da \’yan jarida a garin Jos.
  Ya ce a cikin wadannan gidajen mai da aka rufe, guda 16 an rufe su ne saboda an same su da laifin sayar da man fetur sama da farashin n
  gwamnati, da karkatar da mai a yayin da sauran guda 7 din aka rufe su saboda an samu su da laifin rashin takardar izinin bude gidajen man.
  Cif  Caesar Douglas  ya yi bayanin cewa ‘’a wannan lokaci da muke ci wasu masu gidajen mai, suna kokarin jefa al\’umma cikin mawuyyacin hali ta hanyar sayar da mai sama da farashin gwamnati. Ya ce \’\’amma ina mai bada tabbacin cewa, jami\’an wannan hukuma za su ci gaba da yin iyakar kokarinsu wajen ganin mun yi maganin masu irin wadannan gidajen mai.
  Duk  gidan man da muka kama suna aikata irin wannan laifi za mu rufe 
  wannan gidan man kuma za mu ci su tarar kudi Naira Miliyan biyu\’\’.
  Har\’ila yau ya ce duk gidan man da suka kama da laifin gudanar da aiki ba tare da takardar izini daga hukumar ba, za su rufe wannan gidan man har sai sun zo sun sami takardar izinin gudanar da wannan gidan man.
  Daga nan ya yi kira ga al\’umma kan su kai rahotan dukkan wani gidan mai da suka ga yana sayar da mai sama da farashin da gwamnati ta ce a sayar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here