MATSALAR MAN FETUR TA DAWO A JIHAR KADUNA

  0
  1447

  RABO HALADU, Daga Kaduna


  RAHOTANNI daga Jihar Kaduna  sun bayyana cewa matsalar karancin man fetur ta sake

  kunno kai, inda masu ababan hawa da sauran masu amfani da man ke shan
  wahalar samunsa.


  Jihar kaduna ita ma ta shiga sahun jihohin da ke fama da matsalar inda galibin gidajen mai

  ba sa sayar da man.
  Wasu sun danganta matsalar a kan dilalan man fetur wadanda ba sa son su sayar da man abin da kuma dillalan man fetur din suka musanta.


  Binciken da wakilinmu ya yi  ya gano cewa ana sayar da man ne a kan Naira 100 zuwa 105  a kan kowacce lita, maimakon Naira 87 da
  gwamnati ta kayyade.
  Hukumar kula da rarraba albarkatun man fetur DPR ta gargadi masu gidajen mai da su kauce wa sayar da man fetur fiye da farashin gwamnatin tarayya.
  Hajiya Aisha, Darakta ce a hukumar ta DPR da ke Kaduna ta  bayar da tabbacin  cewa duk gidan man da aka  kama yana sayar da man fetur fiye da farashin gwamnati zai fuskanci fushin hukuma.


  Sai dai su ma a nasu bangaren, \’yan bunburutu masu sayar da man fetur a bayan fage suna cin karansu babu babbaka inda suke sayar da galan daya Naira 700 zuwa 800 wanda hakan ya sanya masu abin hawa sun koka da matsalar man.


  Wani mai mota mai suna  Musa Abubakar da wakilinmu ya  tarar  ya sayi man fetur cikin fushi a wurin \’yan bunburutu ya yi Allah wadai da yadda  masu gidajen man fetur suke sayar da man fiye da farashin gwamnati inda  ya yi  kira ga mahukunta da su dauki mataki domin kawo karshen matsalar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here