An Bayyana Kwazon Gwamna El-Rufa’i A Matsayin Ci Gaban Kasa

0
1774

 

Mustapha Imrana, Daga Kaduna
SHUGABAN jam\’iyyar APC na kasa, Alhaji Bola Ahmad Tinibu, ya bayyana Gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa\’i, a matsayin mutumin da suke sa ran ya ciyar da jaha da kuma kasa baki daya gaba.
Bola Ahmad Tinibu,ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi wajen kaddamar da motocin tasi-tasi guda 200 da za a yi haya da su a Jahar ta Kaduna.
Taron kaddamar da wadannan motoci dai an yi shi ne a filin wasa na dandalin Murtala da ke cikin garin Kaduna.
\”Hakika Gwamnan Jahar Kaduna muna da yakini a kansa zai iya ciyar da kasa gaba don haka ne muka tabbatar sai ya samu wannan matsayi\”.
Ya kuma bayyana Jahar Kaduna a matsayin garin da yake da dimbin tarihin da ake alfahari da shi, don haka dole ne a samu ingantuwar tattalin arziki, tsaro da dai sauransu wanda a halin yanzu ake yin amfani da tsintsiya domin share dattin can baya.
A nasa jawabin Gwamna Nasiru El-Rufa\’i, cewa ya yi wannan shi ne kashi na farko da za a fara daga cikin abubuwan arzikin da za a yi wa jama\’a domin kara inganta al\’amura baki daya.
Ya kara da cewa wadannan motoci kamfanonin Fijo da KiA ne za su bayar da su kuma bankunan Starling da Stambic IBTC ne za su bayar da kudin gudanar da wannan harka.
Kuma za a kammala biyan kudin ne a cikin shekaru 3 wato watanni 36 kenan,sannan duk wanda za a ba wannan motar sai ya ajiye kashi 10 na kudin domin samun ingantar harkar.
 Ya kuma kara da cewa nan gaba kadan za a ga jiragen kasa na tafiya zuwa wasu wurare.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa nan gaba zai kaddamar da motocin haya na bus-bus domin kara inganta harkar sufuri a Jahar Kaduna baki daya.
Shi ma a nasa jawabin shugaban direbobin wadannan motocin Malam Nuhu Bahago, ya bayyana gamsuwarsu da kuma bayar da tabbacin yin amfani da motocin kamar yadda ya dace musamman ta hanyar bin doka da oda.
A nan take an samu motoci 70 a filin kaddamarwar, sauran kuma na nan suna jiran bayarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here