Abokin “Facebook’’ Ya Yanka Mai Masaukinsa

2
2540

 

Imrana Abdullahi, Daga Kaduna
A wani al\’amarin da ke zaman tamkar almara da ya faru a Unguwar Hayin Ruwa, Rigasa shi ne an wayi gari wani yaro da ya ba abokinsa masauki da suka hadu da shi ta sanadiyyar abokantakar dandalin sada zumunta na facebook ya yi wa mai masaukinsa yankan rago.
Kamar yadda budurwar da marigayin mai suna Usaina ta shaida wa majiyarmu cewa shi saurayin nata da zai aureta, ya hadu da abokinsa ta kafar sadarwa ta facebook, kuma har ya taba zuwa wajensa ziyaya a nan Unguwar Rigasa kuma sun je wajenta tare don yin hira.
Usaina ta ci gaba da cewa a wannan ziyarar da suka kai mata shi wanda aka kashen yake gaya wa abokin nasa cewa ga wadda zai aura inda suka dai yi hira bayan sun yi sallama sai suka koma gida tare da saurayin nata.
Amma abin mamaki da bakin ciki sai aka wayi gari aka samu mai masaukin da ya sauke shi a mace shi bakon da aka saukar ya yanke wa wanda ya sauke shi wuya ya kuma fasa masa ciki,ya kuma kwashe duk wani abin amfani mai tsada a cikin dakin da aka sauke bakon.
\”Da akwai wata waya mai tsada da saurayin nawa yake amfani da ita amma sakamakon matsalar rashin cajin da bakon saurayin nawa yake fama da ita sai ya ba shi ya saka layinsa domin yin kira da ita, a wannan lokaci ne muka ji yana cewa oga bisines din da na zo nema ya samu, amma mu ba mu gane me yake cewa ba sai yanzu da lamarin ya faru a haka\”.
Saboda haka ni a matsayina na wadda abin ya shafa nake kira ga daukacin jama\’a da lallai su yi hankali da abokantaka ta facebook don guje wa faruwar irin wannan.

2 COMMENTS

  1. Wannan labarin lallai abin ya zama gargadi ne da kuma matashiya ga masu kokarin cutar da jama’a Allah ya yi mana tsari amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here