SARDAUNAN GORA NAMAYE IKON ALLAH

  0
  2630
  WASU da suke ganin cewa, su mahukunta ne suna ta kokarin raba kawunan al\’umma a kwanakin baya a masallacin Juma\’a
  na Danfodiyo da ke Unguwar Sanusi sun yi iya kokarinsu domin su tozarta Malam Abubakar Gora Namaye a gaban jama\’a kan
  batunkoyarwar da ya gabatar ta yi wa fitaccen halitta Annabi Muhammad SAW salati, to, wannan batu hassada ce wadda Bahaushe
  ke karasa karin maganar da \’taki\’, ta zama taki ga Sardauna.
  Alhaji Abdullahi Mai Awo da ke Malamawa, Kaduna ne ya fadi haka a yayin da yake tattaunawa da wakilinmu a harabar masallacin
  Juma\’a na kan titin Yahaya da ke Malali, bangaren Unguwar Rimi, Kaduna.
  Alhaji Abdullahi ya ce, sam babu tarbiyya ga irin wannan al\’amari da matasan daliban ilimi suke yi, domin da sun fahimci abin da suke
  yi da sai su bari a yi tambaya da bayani don a gane al\’amura, duk da yake masu fahimtar karatu ko koyarwar Malam Abubakar Gora
  suna fahimtarsa kai tsaye ba tare da tangarda ba.
  Ya kuma ce, hassadar da suke yi masa, ai ga shi nan a zahiri, gaba yake yi ba baya ba, domin a masallacin na Danfodiyo, mutum
  nawa ne yake sauraron nasihohin da ake gabatrwa? To, da Malam Gora ya janye daga koyarwar da mu dubbai muke ji,to, ba
  ga shi ba, yanzu yana gabatar da karatuttuka a Rediyo da Talabijin na DITV sau hudu a mako da kuma duk ranakun Juma\’a
  da yake hira da malamai daban-daban na kasar nan, inda kusan mutane miliyan biyu da rabi ke sauraronsa da kallonsa a wannan kafa, ai ka ga wannan hassada da daliban ilimi
  suka nuna masa, Allah Ya nuna ikonSa domin a fahimci al\’amarin ko don a daina hassadar nan ko domin ta zama hujja kan masu karamin sani kukumi ne.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here