Rabo Haladu, Daga Kaduna
KAMFANIN sada zumunta na Facebook zai horas da \’yan majalisar dattawan Najeriya kan yadda ake
yin amfani da shafin sada zumunta.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban majalisar dattawan ta ce hakan zai bai wa \’yan majalisar damar isar da sakonninsu ga \’yan kasar ba tare da matsala ba.
A cewar shugaban majalisar dattawan, Sanata Abubakar Bukola Saraki, mutane da dama na yi wa \’yan majalisar
sojan-gona a shafukan sada zumunta, shi ya sa za a yi musu bita, sannan a \”tantance\” shafukansu domin kawar da matsalar.
Ya kara da cewa jami\’an kamfanin na Facebook ne za su dauki nauyin koyar da \’yan majalisar dattawan,
don haka majalisar ba za ta kashe ko sisi ba.
Shafin sada zumunta na facebook yanzu ya zama wata kafa da al\’ummar Najeriya suke yada manufofinsu mabambanta a kodayaushe.