BABBAN daraktan yan agaji na kasa na kungiyar Jama\’atu Izalatul Bid\’a Wa\’iqamatis Sunna (JIBWIS),Malam mustapha Imam Sitti, ya bayyana cewa sakamakon aiki tukuru na sa kai da kuma daukar matakan tsaro sun bayar da damar damke wani da ake zargin cewa shi dan kungiyar Boko Haram ne.
Daraktan yan agajin ya shaidawa manema labarai cewa an canke shi ne a sanye da kayan agajin kungiyar wato dai wadanda aka fi sani da \”yan agaji\” an kuma same shi ne yana nuna wa kamar shima dan agaji ne irin na wannan kungiya ta agajin sa kai.
\”hukumar sojojin najeriya sun horar da yan agaji ta yadda za su gane junansu a duk inda suke yin aiki a duk fadin tarayyar kasar baki daya,don haka ta hanyar amfani da wadannan alamomi mambobinmu za su iya gane kawunansu a duk inda suka samu kansu.Ta haka ne aka damke wanda ake kira Usman, da tuni aka mika shi a hannun jami\’an tsaro,\” inji Sitti
Sitti ya kuma kara da cewa da akwai wani lokacin da aka kashe wani dan agaji a karamar hukumar Soba, ta hanayar sarar sa da adda don haka ya tabbatar mana da cewa Boko haram ne suka halarkar da shi.
Da yake tabbatar da faruwar wannan al\’amari babban jami\’in rundunar yan sanda shiyyar Zariya Muhammad D.Shehu,ya bayar da shawara ne ga jama\’a da su kula da kawunansu musamman a wuraren Ibada,kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama\’a saboda gudun yadda yan kungiyar Boko Haram ka Iya kai masu hari.
Imrana Abdullahi daga Kaduna.