RABO HALADU, KADUNA
Rundunar \’yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da cewa wani mutum ya kashe \’yayansa hudu sannan ya yanka kansa a unguwar Kawo.
Rahotanni dai na cewa rigima ce tsakanin miji da matarsa ta haddasa rasuwar \’ya\’yan ma\’auratan gudu hudu.
Ana zargin mutumin da yi wa \’ya\’yansa — mace daya da maza uku yankan-rago, saboda zargin da ya yi cewa matarsa na yunkurin dauke su ta gudu da su.
A yanzu dai wanda ake zargin na kwance a asibiti rai a hannun Allah sanadiyyar yankan da
ke wuyansa.
Rundunar \’yan sanda ta ce an sami rubutaccen bayanin da mutumin da ake zargi ya yi, inda ya ce \”kaddara ce tasa ya dauki matakin saboda haka yana fatan zuwa Aljanna domin hutawa da matsalolin rayuwar duniya\”.