An sace man fetur na biliyan 50 – NNPC

  0
  1275

  Usman Nasidi Daga Kaduna

  Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, ya ce an yi asarar lita miliyan
  531 na man fetur wanda kudinsa ya kama naira biliyan 50, sakamakon
  barnar da barayin bututun mai suka yi tsakanin watannin Janairu da
  Satumbar 2015, a wasu layukan bututu da aka shimfida su daga jihar
  Legas zuwa birnin Ilorin.

  A wani jawabi da ta gabatar a gaban kwamitin man fetur na majalisar
  dattawan kasar, Manajan Daraktar hukumar kula da bututun mai na
  kamfanin PPMC, uwargida Esther Nnamdi Ogbue, ta ce asarar da aka samu
  ta faru ne sakamakon fashe-fashen bututun man fetur a yankunan Arepo
  da Mosimi, wanda hakan ya sanya ake samun matsalar fitar da man.

  Uwargida Nnamdi-Ogbue ta ce duk da
  kalubalen da ake fuskanta a layukan bututun da aka shimfida daga Lagss
  zuwa birnin Ilorin din, PPMC zai ci gaba da kokarin tabbatar da cewa
  kasar ta samu isasshen man fetur din da ake bukata wajen loda mai daga
  daffo din dake Lagos da Oghara da kuma na baya-bayan nan da ke
  Calabar.

  Kazalika, Shugabar hukumar PPMC ta kara da cewa wasu dillalan mai
  marasa kishin kasa ne ke dakile kokarin da hukumar ke yi na kawar da
  layuka a gidajen mai a fadin kasar, inda suke ayyukan da basu dace ba,
  kamar sayar da man a kasuwannin bayan fage.

  Hukumar ta tabbatar da cewa tana duba hanyoyin da za ta bi wajen
  tabbatar da cewa an samu mafita ta din-din-din ga wannan matsala ta
  rashin mai, inda ta ce akwai bukatar a gina wani rumbu na adana
  isasshen man fetur.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here