Kasar Saudiyya na shirin fille kan wasu mutane 50

0
1395

Kungiyar kare hakkin bil adama, Amnesty International ta ja hankalin
al\’umma game da rahotannin da ke cewa hukumonin Saudiyya na shirin
yanke hukuncin kisa kan mutane da dama a rana guda.

Jaridar Okaz ta ce mutane 55 ne da ake zargi da aikata laifukan
ta\’addanci ke jiran wannan hukunci, amma wata jaridar mai suna al-
Riyadh ta ce mutane 52 ne.

A cikin wadanda za a yanke wa hukuncin har da mabiya Shi\’a wadanda
suka yi zanga-zangar adawa da gwamnati.

Amnesty ta ce ganin yadda yanke hukuncin kisa ya karu a kasar a bana,
dole ta dauki rahoton da muhimmanci.

Kungiyar ta ce a kalla mutane 151 aka kashe a Saudiyya a wannan
shekarar, wanda ba a taba samun yawan hakan ba tun shekarar 1995.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here