Isah Ahmed Daga Jos
Ministan kasa a ma\’aikatar harkokin sufurin jiragen sama ta tarayya,
Sanata Hadi Sirika ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata farfado da
harkokin sufurin jiragen sama a Nijeriya.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron harkokin sufurin jiragen sama
na duniya, da aka gudanar a birnin Montreal, na kasar Kanada.
Ya ce wannan gwamnati ta Nijeriya, karkashin shugaban kasa Muhammad
Buhari ta kuduri aniyar sake farfaxo da harkokin sufurin jiragen sama
a Nijeriya, ta hanyar gyara tashoshin jiragen saman kasar da tare da
samar kayayyakin aiki irin na zamani a tashoshin.
Ya ce gwamnatin Nijeriya zata yi hakan ne don ganin ta tafi tare da manyan kasashen
duniya, da suka cigaba kan harkokin sufurin jiragen sama.
A nasu jawaban daban daban a wajen taron ministan sufuri na kasar
Kanada Marc Garneau da ministan sufuri na kasar Kolombiya da sakatare
janar na kungiyar yawon bude ido ta duniya [UNWTO] sun bukaci
kasashen duniya su hada kai, don ganin an aiwatar da tsare tsare
bunkasa harkokin sufurin jiragen sama a duniya, don amfanin al\’ummar
duniya.
Shi dai wannan taro ministan kasa a ma\’aikatar sufurin jiragen sama ta
tarayya Sanata Hadi Sirika ne ya jagoranci tawagar Nijeriya, wadda ta
kun shi jakadan Nijeriya na riko a kasar Kanada Jafar Mohammed da
daraktocin ma\’aikatar harkokin sufurin jiragen sama ta Nijeriya kuma taron ya sami halartar wakilai daga kasashen duniya 99.