GWAMNAN Jahar Kaduna malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ya kara tabbatar wa da daukacin al’ummar jahar cewa har yanzu yana nan a kan bakansa na ciyar da jahar gaba.
Gwamna El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2016 ga majalisar dokokin jahar.
Kasafin kudin na kimanin Naira biliyan 171 ya samu halartar jama’a da dama daga cikin jahar musamman masu ruwa da tsaki a kan tafiyar da al’amura.
Ko a satin da ya gabata sai da gwamnan ya kira taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan harkokin jahar domin tattaunawa a kan batun kasafin kudin shekarar 2016 mai zuwa,inda jama’a da dama suka tofa albarkacin bakinsu tare da bayar da shawarwari wanda dalilin hakan yasa gwamnatin ta yi kari kadan a kan abin da ta fito da shi tun da farko da niyyar za ta kasafa a can baya na kudi Naira biliyan 166 amma sakamakon yin taro da jama’a a gidan tunawa da marigayi Hassan Usman Katsina aka samu karin da ya kai kasafin kudin Naira biliyan 171.
“Mun yi kamfe a game da batun matsalolin da suka shafi makatantu,asibitoci,hanyoyi da rashin aikin yi wanda ake bayyana wa da cewa shi ne ya haifar da rashin tsaron da ake fama da shi,wannan batun matsaloli yasa a yanzu mun dukufa domin ganin bayansu baki daya ta yadda jama’a za su samu walwala da tafiyar da harkokinsu na yau da kullum”.