Imrana Abdullahi Daga Kaduna
BAYAN harin bam din da aka kai wa jerin gwanon yan uwa musulmi mabiya shi\’a da ya kashe mutane da yawa a lokacin da suke kan hanyarsu daga kano zuwa Zariya domin halartar taron da jagoran shaikh Ibraheem Yakubu El-zakzaky,zai jagoranta.
Jagoran na yan uwa musulmi mabiya shi\’a ya bayyana cewa babu wani abu wai Boko haram da har ake cewa su suka kai harim kamar yadda kafafen yada labarai suka rika yadawa a duniya.
Kamar yadda mai magana da yawun mabiya shi\’ar Ibrahim Usman,ya bayyana cewa yaji shugaban na cewa \”Mun san wadanda aka ba da wadanda suka bayar da kwangilar ayi wannan aikin na kisan yan uwa musulmi, saboda ba wasu boyayyun mutane bane a gare mu. Don haka babu wani zancen Boko Haram don haka sai dai su gayawa wadanda ba su sani ba. ya dace su sani cewa suna yi ne da wadanda suka san addini,masu ilimi tare da hangen nesa\”.
Kamar yadda takardar bayanin ta bayyana shugab na yan shi\’a ya bayyana haka ne a lokacin karatun Nahjul Balagha da aka yi a cibiyar Hussainiyya Baqiyyatullah a garin zariya a ranar litinin.
Sheikh zakzaky ya karta cewa wai wani abu ne Boko haram kamar yadda kafafen yada labarai suka rika yayata wa a ranar Juma\’a inda ya ce an shirya shi ne kawai kuma ake kokarin boyewa jama\’a gaskiyar lamarin ana fadin wai boko haram ne wani boyayyaen abu ta hanyar kai harin Bam.
Kamar yadda ya bayyana cewa an yi amfani da kafafen yada labarai ne domin kawai ace wai Boko haram ne suka kai harin.
\”Babu wani abu mai kama da harin bam.an dai yi amfani da wasu ne da aka ba su kayan maye suka dauki abin fashewa suka kuma yi amfani da shi a cikin jama\’a\”.
a wa Allah arinka fadar ko waye ke da hannu kai irin wannan kisan. Allah kawar mana da duk mai hannu a taaddanci.