TSOHON shugaban jam\’iyyarf PDP na kasa Alhaji bamanga tukur ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wadansu mahara suka kai masa hari a kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman garin Abuja.
Bayanai sun bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da yake kan hanayarsa ta zuwa garin Owerri daga Abuja domin zuwa jami\’ar gwamnatin tarayya ta fUTO a jahar IMO da ta ba shi digirin girmamawa.
Motocinsa guda hudu da suke cikin jerin gwanon motocinsa sun ki amincewa da bayar da dama ga maharan su kutsa cikinsu wanda sakamakon hakan ya tsallake rijiya da baya.
IMRANA ABDULLAHI Kaduna.