Makarantar kiwon lafiya Ta Saminaka Ta Ya Ye Dalibai 136

0
1868

Isah Ahmed Daga Jos

Makarantar koyon aikin kiwon lafiya ta Kungiyar malaman makarantun Kungiyar darikar Tijaniya dake garin Saminaka a jihar Kaduna, ta gudanar da bikin yaye dalibanta karo na biyu, a inda ta ya ye dalibai guda 136  a ranar lahadin da ta gabata.

Da yake jawabi a wajen taron, Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya bayyana cewa wannan taron  yaye dalibai da wannan makaranta ta shirya, wani gagarumin taro  ne, saboda mahimmancin da makarantar take da shi a  wannan yanki.

Ya ce babu shakka irin wadannan makarantu sune matakan cigaban kasa. \’\’Muna  godiya ga irin wadannan makarantu  kan irin kokarin da suke yi wajen ilmintar da matasan wannan yanki. Muna kira ga al\’ummar wannan
yanki  su cigaba da baiwa wannan makaranta da sauran irin wadannan makarantu  goyan baya da hadin kai, ta hanyar  tallafa masu\’\’.

Ya yi kira ga al\’ummar kasar nan   su tashi su rungumi harkokin neman ilmi, domin idan suka rungumi harkokin neman ilmi duk irin rigingimun da ake samu a kasar nan  za a magance  su.

Shima a nasa jawabin shugaban riko na karamar hukumar Lere Alhaji Sani Tanimu Saminaka ya bayyana cewa wannan karatu da wadannan xalibai suka yi, wani mataki ne na taimakon al\’umma. Don haka ya yi kira a garesu
su yi  kokari su taimakawa al\’umma kan harkokin kiwon lafiya.

Shugaban rikon wanda Malam Sunusi Sufiyanu ya wakilta ya ce a shirye gwamnati take ta tallafawa wadannan dalibai da suka kammala wannan karatu, domin su taimakawa al\’umma.

Ya ce gwamnati zata cigaba da tallafawa harkokin kiwon lafiya da sauran fannonin kyautata rayuwar al\’umma, domin taimakawa al\’umma.

A nasa jawabin shugaban makarantar Malam Muhammad Auwal Bin Usman Saminaka ya ce sun shirya taron domin su ya ye dalibansu karo na biyu.
Ya ce a wannan karo mun ya ye dalibai guda 136 wadanda suka kammala karatun bayar da gudunmawa kan kiwon lafiya.

\’\’A gaskiya mun sami nasarori da dama sakamakon bude wannan makaranta, domin dalibanmu da dama an dauke su aikin gwamnati a wannan yanki, wasu sun tafi manyan makarantu wasu kuma suna nan suna tallafawa al\’umma kan harkokin kiwon lafiya a wannan yanki.\’\’

Ya yi  kira ga matasan wannan yanki su zo su shiga wannan makaranta don cin gajiyar abubuwan da ake horarwa a makarantar, don a taru a taimakawa harkokin kiwon lafiya a wannan yanki da kasa gabaki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here