NCC Ta Rage Tarar Da Ta Yi Wa MTN

  0
  1384

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  Hukumar da ke sanya ido a kan kamfanonin sadarwa a Najeriya, NCC ta rage tarar da ta ci MTN daga $5.2bn zuwa
  $3.4bn.
  Hakan dai na nufin an rage tarar da kusan ninki uku kuma hakan na kunshe ne a cikin   wata sanarwa da kamfanin na MTN ya fitar,inda ya ce hukumar NCC ta bukace shi ya biya tarar kafin karshen watan Disamba.
  Kamfanin ya ce zai fara tattaunawa da NCC nan take domin duba yiwuwar fara biyan tarar.
  A watan Oktoba ne NCC ta sanya wa MTN tarar $5.2bn saboda ya ki yanke layukan mutanen da ba su yi rijista ba har wa\’adin da aka diba domin yin rijistar ya wuce.
  MTN shi ne babban kamfanin sadarwa a Najeriya, kuma ana ganin \’yan ta\’adda na yin amfani da layukan wayoyi domin tsara kai hare-hare.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here