Kisan Kai Ba Da Niyya Ba An Yanke Wa Hadiza Hukuncin Kisa

0
1912

Rabo Haladu Daga Kaduna

Kotu a Ingila ta yanke wa Dr Hadiza Bawa-
Garba, daurin hukuncin je ki gyara halinki
na shekaru biyu, saboda samun ta da laifin
kisan kai bada niyya ba.
Haka kuma kotun ta yanke wa Isabel Amaro
hukunci iri daya da Dr Hadiza, saboda samunsu
da sakacin aiki abin da ya janyo rasuwar Jack
Adcock, dan shekaru shida a wani asibiti da ke
birnin Leicester.
A lokacin yanke hukuncin, mai shari\’a Andrew
Nicol ya ce sakacin ma\’aikatan asibiti su biyu
ya janyo \”mutuwar Jack cikin kankanin lokaci\”.
Jack Adcock wanda ke fama da ciwon maloho
da kuma matsalar zuciya, ya rasu ne a wani
asibiti da ke Leicester a watan Fabarairun
2011.
Dr Hadiza Bawa-Garba \’yar asalin Nigeria ce,
iyayenta ne suka turo ta Ingila karatu kuma ta
samu shaidar zama likita a makarantar koyan
aikin likita ta Leicester Warwick.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here