KOTUN daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke a game da zaben gwamnan Jahar Rivers da gwamnan da ke kan kujerar ya ce daukaka tun bayan da kotu ta yanke masa hukunci.
Kotun a yau ranar laraba ta bayyana cewa Nyeson Wike,da ya tsayawa jam\’iyyar PDP takara a zaben da ya gabata bai ci zabe ba.
Kotun sauraren kararrakin zaben tun a ranar 24 ga watan okutoba ta rushe zaben da Nyeson Wike na PDP ya ce an yi masa kuma kotun da ke zamanta a abuja ta bayar da umarnin a sake wani zabe.
Amma tun bayan da aka yanke wannan hukunci sai ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara yana kalubalantar wancan hukunci.
Zaben gwamnan Ribas da ya gabata ya sha suka daga ciki da wajen Najeriya musamman ga wadanda suka sanya idanu a lokacin zaben,wanda kuma bayan kammalawa da kuma lokacin da ake yinsa aka yi ta faman rikici.
Imrana abdullahi kaduna