Rashin Ilimi Ya Haifar Wa Fulani Matsala – Sarkin lere

0
2687

Isah Ahmed Daga Jos

Mai martaba Sarkin Lere da ke jihar Kaduna Birgediya Janar Garba Abubakar Muhammad mai ritaya ya bayyana cewa rashin ilmi ne, ya sanya ake yawan cin zarafin al\’ummar fulani a kasar nan.

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da shugabannin wata sabuwar kungiyar matasan fulani, mai suna Bandiraku Fulbe a fadarsa da ke garin Lere.

Ya ce  saboda rashin ilmi, idan fulani suka je wajen kiwo aka sami matsala, sai a ci mutumcin su a kashe su kuma  babu wani abin da za a yi. Ya ce babu shakka Ilmi ne zai dawo da martabar al\’ummar fulani a kasar nan.

\’\’Yanzu ilmin boko ya zama mahimmin abu ga al\’umma. Don haka ina kira ga al\’ummar fulani  su rika gina makarantun islamiyya, don su sanya \’yayansu tun suna kanana kuma su sanya su a makarantun boko\’\’.

Ya yi kira ga  shugabannin  wannan kungiya su rike aikin  da aka basu, kuma su mayar hankali kan ilmi, ta hanyar  wayar da kan al\’ummar fulani wajen sanya yara a makarantu.

Mai martaba Sarkin Lere ya yi bayanin cewa saboda mahimmancin da masarautar Lere ta baiwa harkokin ilmi, shi da kansa da Hakimansa da dagatansa da masu unguwanin   masarautar zasu bi gida gida, don ganin an kai dukkan yaran masarautar makarantu. Ya ce dole ne  a saka kowanne yaro a makaranta a wannan masarauta.

Shi ma  a nasa jawabin babban bako mai jawabi kuma tsohon shugaban karamar hukumar Lere, Alhaji Ibrahim Abdulkarim Lazuru ya bayyana ce al\’ummar fulani basa saka sheda a dukkan wuraren da suke zama. Ya ce da al\’ummar fulani suna saka sheda a dukkan wuraren da suka zauna, da ba su sami kansu a cikin matsalolin wuraren zama da suke fuskanta ba a halin yanzu.

Ya yi kira ga gwamnati kan idan zata kafawa fulani wuraren kiwo,  ta samar da abubuwan more rayuwa kamar ruwan sha da wutar lantarki da hanyoyin mota, a wuraren. Ya ce yin haka  zai sa fulani su rika zama a wuri daya.

Daga nan ya yi kira ga  al\’ummar fulani su rungumi harkokin neman ilmin addini da ilmin  boko.  Kuma  su rika sanya \’yayansu a wuraren koyon sana\’o\’in hanu.

Tun da farko a nasa jawabin shugaban kungiyar Abbas Jafaru Julde ya bayyana cewa babban kudurinsu kan kafa wannan kungiya shi ne hada kan al\’ummar fulanin yankin karamar hukumar Lere tare da  bunkasa ilminsu.
Don haka ya yi kira ga al\’ummar fulani kan su basu goyan baya tare da addu\’a don ganin sun cimma nasara kan wannan aiki da suka sanya a gaba.

Shi dai wannan taron kaddamar da shugabannin wannan kungiya, ya sami halartar hakimai da ardodi da sauran shugabannin al\’ummar fulani daga kowanne bangare na jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here