Daga Usman Nasidi
A makon jiya ne aka zargi wata mata mai suna Safina, matar Malam Adamu Yawale, da suke zaune a Unguwa Uku a garin Gombe da laifin kashe danta mai suna Hafiz, mai shekara da wata biyu da haihuwa.
A lokacin da al’amarin ya faru, wakilinmu ya yi kokari don ganin matar ya ji ta bakinta kan wannan zargi da ake mata ganin duk da irin son da uwa take yi wa dan ta amma a ce ta sa wuka ta fille masa kai, amma al’amarin ya
faskara; domin daga faruwar lamarin ’yan sanda suka kama ta suka tsare.
Wakilinmu ya yi kokari ya samu jin ta bakin mijin matar Malam Adamu Yawale ta wayar salula, inda ya tabbatar da hakan sannan ya ce wannan al’amari mukaddari ne daga Allah.
A cewarsa, a wannan rana da wannan iftila’i zai faru ya bar yaron da mahaifiyarsa a gida lafiya har ta ba shi shayi ya sha sannan ya biyo shi jikin babur dinsa kirar Bespa.
Ya ce a lokacin da yaron mai suna Hafiz ya biyo shi jikin babur sai ya ce masa, to ya koma gida zai fita sai ya dawo, ita uwar ce da kanta ta zo ta dauki yaron. Ya ce yadda suka rabu da su a gidan ke nan sai ya dawo ya tarar da gawarsa.
Ya kara da cewa a lokacin da matar ta sare kan yaron sai jama’a suka kai wa ’yan sanda rahoto, su kuma suka zo suka kama ta suka tafi da ita ofishinsu don bincikarta.
Ya tabbatar da cewa matarsa Safina tana da tabin hankali wanda ya same ta kafin Sallar Layya, inda a lokacin ne suka fara gane cewa ta hadu da aljannu, sai dai ba su iya yin komai a kai ba saboda ba ta taba aikata wani mummunan al’amari ba.
Yace “Wannan yaro da ta kashe, ba shi ne babban dan da muka haifa da ita ba, ’ya’yanmu uku, daya ya rasu. Shi ma Hafiz ga yadda ta kasance da shi yanzu saura danmu daya a raye.
Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’yan sandann Jihar Gombe, DSP Fwaje Atajiri ya tabbatar da cewa matar tana wajensu amma suna kan bincike, idan an kammala za a mika ta gaban kotu.