Daga Usman Nasidi
Iyalan wani matashi mai suna Muhammad Abubakar da aka fi sani da Babani dan kimanin shekara 36 da yake zaune a Unguwar Kaji a
garin Potiskum a Jihar Yobe suna zargin wani
babban dan kasuwa mai harkar fetur a garin da
hallaka dan uwansu, bayan da ya dauke shi zuwa kasar Indiya don a cire kodarsa a dasa wa dansa mai suna Paris.
Marigayi Babani wanda ke da matan aure biyu
da ’ya’ya tara, ya rasa ransa ne bayan da dan
kasuwar mai suna Alhaji Husaini Ibrahim
wanda yayi fice a harkar man fetur kuma yake da gidajen mai da dama a garin Potiskum ya dauke shi zuwa kasar Indiya ba tare da sanin
danginsa ba aka cire kodarsa don dasa wa
dansa Paris a kasar Indiya.
Wani shakikin marigayin mai suna Alhaji
Ahmad Mustapha ya bayyana cewa, dan uwansu Muhammad Babani sun yi sallama
da shi a ranar Talata 10 ga watan Nuwanban da
ya shige cewa zai je ziyara Kaduna wurin
abokinsa, to daga nan ba su sake jin labarinsa
ba sai ranar 20 ga Nuwamban aka kira shi a
waya da yamma cewa Alhaji Husaini Yunusa ya
zo gidansu da kannensa biyu shi ne sai ya tafi
gidan.
Ya ce, “Bayan da na je gidan sai na tarar da
Alhaji Husaini zaune a falon malaminmu shi da
wasu mutum hudu da ya zo da su. Sai Alhaji
Husaini ya tambaye ni ko ina da labarin
Babani? Na ce lallai ina da labarinsa, don ya ce
min ya yi tafiya zuwa Kaduna. Sai Alhaji Husaini
ya ce kanenku tafiyarsa ta yi nisa don ya bar
Najeriya zuwa kasar Indiya. Sai na ce kamar
yaya? Sai ya ce ai Babani sun tafi da ’ya’yansa
biyar zuwa kasar Indiya domin akwai dansa
marar lafiya mai suna Paris da ke da ciwon
koda da nufin Muhammadu (Babani) ya amince
a ciri kodarsa a dasa wa Paris a matsayin
taimako.”
Alhaji Ahmadu ya kara da cewa da ya ji haka,
sai ya tambayi Alhaji Husaini cewa, yaya aka yi
haka ba tare da sanin kowa ba? “Mu ga abin da
ya fada mana cewa za shi Kaduna ne ziyara,”
inji shi. A nan sai Alhaji Husaini ya ce shi
Muhammadu Babanin ne ya ce kada su fada wa
kowa, shi ne suka rufe maganar ba su fada wa
kowa ba suka yi tafiyarsu kasar ta Indiya har
haka ta kasance.
Da suka tafi kasar Indiya da kwana takwas don ba da kodar ne sai kuma Allah Ya yi masa cikawa. A nan sai na ce to yaya za a yi a ce an tafi da shi kasar Indiya don ya ba da koda ba tare da sanin ’yan uwansa ba, ai wannan zance ne kawai babu maganar taimako tunda ba dan uwansa ba ne ba kuma danginsa ba ne, sai dai inda kudi kuka rude shi,” inji Alhaji Ahmad.
Ya kara da cewa bayan mako daya a ranar
Alhamis aka kawo musu gawarsa garin
Potiskum, sai suka je caji ofis inda DPO na
Potiskum ya sa aka dauki jawabinsu da na
Alhaji Husaini sai ’yan sanda suka ce a sa shi
Alhaji Husaini a bayan kanta. Daga bisani sai
DPO ya sa a gwada gawar don sanin ainihin
abin da ya faru.
“Kuma daga nan sai muka tafi Damaturu wajen Kwamishinan ’Yan sanda, amma sai muka ga Kwamishinan yana jan kafa a kan wannan abu. Saboda muna ganin Alhaji Husainin na gadara da dukiya, kuma ana cikin haka ne sai wani daga cikin ’ya’yan Alhaji Husainin ya ce mu yi hakuri mu je gida za mu sasanta a kuma yi jana’izar marigayin.
To wannan abu shi ya faru don haka mu ’yan uwan marigayi Muhammad Babani ba mu yarda da wannan abu na rasuwar dan uwanmu ba a hannunsu ba, kuma muna fata hukuma za ta bi mana hakkinmu,” inji Alhaji Ahmad.
Da aka tuntubi Alhaji Husaini Ibrahim mahaifin Paris matashin da ke fama da jinyar koda har aka tafi da marigayin kasar Indiya don cire tasa, dangane da wannan zargi da ’yan uwan marigayi Babani ke yi cewa ya dauki dansu zuwa kasar Indiya ba da saninsu ko amincewarsu ba kuma ya rasu a can?
Sai ya ce, ya san zai mutu ya gamu da Allah, amma a iya saninsa ya san marigayin da kansa ya tafi Kano lokacin da dansa Paris na kwance a asibiti a Kano yana jinya, da ya je ganinsa sai ya ce wa Paris tunda ciwon koda ne ke damunka in zai yiwu zan ba ka tawa kodar guda daya, sai ya ce to in har za ka ba ni ai yana da kyau.
Alhaji Hussaini Yunusa wanda fitaccen mai
harkan man fetur ne da gidajen mai a garin
Potiskum kuma ya kara da cewa, sai marigayin
ya ce wa dan nasa to amma ya ba shi lokaci, to
bayan wata biyar sai marigayin ya sake dawowa
wajen Paris ya ce masa, ya shirya yanzu zai ba
shi koda, sai Paris ya ce masa to bari ya fada
wa mahaifina. Sai marigayi Babani ya ce in zai
fada to ya fasa don sai a yi ta gulmarsa a ce ya
karbi kudi ya sayar da kodarsa.
Alhaji Husaini Yunusa ya ce, “Haka aka rika
rufa-rufa don kada in sani, saboda in har na
sani dole sai na tuntubi iyalensa kafin a tafi da shi, amma duk haka na yi ta matsa lamba a kan sai an sanar da iyalensa amma marigayin ya kekasa kasa ya ce in har sai an fada wa ’yan uwansa to shi zai fasa taimakawa, haka aka yi ta fama daga karshe suka je suka yi biza suka hau jirgi suka tafi kasar Indiya.
Bayan su isa kasar Indiya ne da kwana daya tun kafin a yi aiki aka yiwo masa waya cewa, Muhammad Babani ya rasu. To ka ga ba a ma ciri kodar ba Allah Ya yi masa rasuwa.”
Ya ce yanzu haka mahaifiyar dan nawa tana
shirye-shiryen tafiyar kasar Indiya don ba da
koda ga danta. Wannan shi ne gaskiyar
magana.
A nashi jawabin, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe, Alhaji Muhammad Zanna Ibrahim a kan lamarin cewa yayi, wannan magana tana nan a hannun jami’an bincike tukunna.