Gwamnatin Buhari Ta Rage Farashin Man fetur

  0
  1616

  Daga Usman Nasidi

  Karamin Ministan man fetur na kasar Najeriya, Dakta Emmanuel Ibe Kachikwu ya bayyana cewa gwamnatin kasar nan ta yanke hukuncin rage farashin man fetur daga Naira 87 zuwa 85 a kowace litar man a shekara mai zuwa.

  Ministan wanda ya bayyana haka, yayin wata
  tattaunawa da ya yi da \’yan jarida a Fatakwal,
  babban birnin jihar Rivers, ya ce ragin zai fara ne daga ranar daya ga watan Janairun sabuwar shekara.

  A cewar Ministan, gwamnati ta dauki wannan
  matakin ne bayan da ta yi nazarin hawa da saukar da farashin mai ke yi a kasuwar duniya.

  A baya dai gwamnatin Najeriya ta sha alwashin cewa za ta dinga yanke farashin mai gwargwadon yadda yake a kasuwar duniya.

  Haka kuma ta dauki matakin rage fashin ne don tabbatar wa da \’yan Najeriya cewa babu
  yaudara a cikin batun.

  Hakazalika, Ministan man fetur din ya umarci hukumar sayar da albarkatun manfetur da ta sanya takunkumi kan gidajen man da ke boye mai.

  A wata sanarwa da kakakin kamfanin man na
  NNPC, Ohi Alegbe ya fitar ya ce Mista Kachikwu ya bayar da umarnin ne a lokacin da ya kai wata ziyarar gani da ido zuwa wasu gidajen man.

  Sanarwar kuma ta kara da cewa a ranar Laraba ministan zai gana da dukkannin masu ruwa da tsaki a harkar mai da dakonsa a kasar Najeriya.

  Ada dai Wasu sassa na kasar Najeriya sun dade suna fama da matsalar rashin man, kamin daga  baya bayan nan ne matsalar ta kuma kunno kai a garin Abuja, babbar barnin tarayya kasar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here