BABBAN dalilin da yasa mai rubutu ya ce lallai ya dace jama\’a su yi koyi da sanata shehu sani,mai wakiltar al\’ummar kaduna ta tsakiya shi ne irin yadda yake ci gaba da daukar nauyin kulawa da marasa galihu da suke cikin jama\’a musamman irin yadda yake kokarin ganin duk mutumin da yake neman wani hakki da lamarin ya yi masa nisa to da yazo wajen Sanata Shehu sani zai samu waraka cikin yaddar Allah.
A wata rana ne wadansu dalibai musulmi da suke yin karatun jamai\’a daga jami\’ar Ahmadu bello Zariya masu karatun aikin lauya suka zo ofishinsa da ke layin katsina cikin garin kaduna suka koka masa da cewa suna son ya taimaka ya yi magana a majalisar dattawa ta kasa kan a duba irin yawan kudin da dalibai ke biya duk likacin da suka kammala karatun jami\’a suka je makarantar koyon aikin lauya ta kasa.
A bin farin ciki sai ga wannan Sanata Shehu Sani ya tashi a doron majalisar dattawa ta kasa ya yi bayani sosai a kan wannan lamari tare da nunawa majalisar cewa ya dace a duba saboda da akwai yayan talakawa da yawa wadanda idan sun kammala karatunsu suke fama da yawan kudin wannan makaranta.
Abu na biyu kuma shi ne irin yadda a kwanan baya ya dauki nauyin karatun yayan wani sojan Najeriya su shida da aka kashe a Jahar Barno da aka kai su domin yin yaki da yan Boko Haram,ya kuma samu wannan labarin ne ta hanayar kafar sada zumunta ta FACEBOOK inda wani daga cikin abokan wancan marigayi sojan Najeriya ya bayyana irin halin da yayan suke ciki na kunci duk da cewa ubansu ya rasa ransa ne a wajen yaki domin kasa ta ci gaba.
Sai kuma irin yadda ya dauki nauyin wadansu yara 2 marayu da suka kammala karatun sakadare ya dauki nauyinsu har sai sun kammala karatun jami\’a kuma wani gata ma shi ne a kasar Chaina wanda kowa ya sani yin karatu a wata kasa a nan Afirka ma ba karamin al\’amari bane balantana a kasar mai nisa haka kuma har a kammala karatun jami\’a ga maraya mara galihu da ake yin watsi da su amma sai ga sanatan sanatoci shehu na Allah sanannen dan gwagwarmayar kwato yancin talaka da ya dade a kan irin wannan aiki domin ganin rayuwar talakawa ta inganta ya rungumi abin da idan a can baya ne za\’a ce ba zai yuwuba.
Kuma idan aka dawo ga aikin majalisa kowa ya sani ba\’a taba samun Sanatan da yake wakiltar jama\’a daga jahar Kaduna yake bayani tare da kawo kudiri a majalisar Dattawa kamar sa ba,indai ana bibiyar lamarin kuma za a yi domin Allah. Saboda sanata Shehu Sani ya zama abin da za a yi koyi da shi a inganta rayuwar dan Adam a cikin al\’umma baki daya.
Imrana Abdullahi ne ya rubuta wannan makala.