Mun Dakatar Da Sanata Shehu Sani Tsawon Watanni 11-Mazabar T/Wada

  0
  1588

  LALLAI abisa dukkan alamu wadanda suka rubuta wannan takardar kora ba su san kundin tsarin mulkin APC da kuma dokokin zabe ba.

  Wadannan sune irin kalaman da suke fita daga bakunan yayan APC musamman magoya bayan Sanata mai wakiltar mazabar kaduna ta tsakiya sanata Shehu Sani,tun bayan da suka samu wata takardar da ta bayyana a ofishin sanatan da ke kusa da filin wasa na Ahmadu Bello da ke cikin garin kaduna.

  Takardai tana dauke da sa hannun sannun wasu daga cikin shugabannin APC daga mazabar sanatan da ke Tudun Wada kaduna sunan mazabar itace kamar haka Tudun Wada ta Arewa mazaba ta 6 na dauke da sunayen mutanen da suka sa mata hannu  kamar haka Ahmed Abdullahi sakatare,Auwalu Mai Anguwa jami\’in yada labarai da Aminu Alilan na dauke da kwanan wata kamar haka 27-12-2015.

  Kamar yadda mai bayar da shawara a kan harkokin siyasa da kuma akida Suleiman Ahmad,ya shaidawa manema labarai cewa suna sane da cewa su wadannan shugabannin APC tun daga mazaba suna yi wa gwaman nasiru El-Rufa\’i aiki ne kawai.

  \”Kuma muna sane da cewa suna yin haka ne domin kawai shi Sanata Shehu Sani,yana yin bayani a kan irin yadda ake gudanar da ayyukan da jama\’a basa so a jahar kaduna da sunan APC ta zabi masu mulki.

  Takardar mai dauke da kwanan wata 27-12-2015 na cewa bayan mun kammala taro a wannan rana a mazaba ta 6 ta karamar hukumar kaduna ta kudu an cimma yarjejeniya kamar haka.

  1.kalaman da Sanata shehu Sani ya yi a kwanannan sun sabawa tsarin APC a matsayin jam\’iyya.

  2.Sanatan ya kuma yi nasarar raba kawunan yan jam\’iyya.

  3.irin ayyukansa sun yi wa jam\’iyya kafar Ungulu musamman ayyukan gwamna nasiru Ahmad El-Rufa\’i duk saboda kalamansa da yake yi a bayyane.

  4.Babu ta yadda za a hada sati guda mutanensa ba su yi magana a kafafen yada labarai ba suna kalubalantar ayyukan gwamna nasiru Ahmad El-Rufa\’i.

  5.kalamansa a matsayin kasa sun sabawa tsarin malam Nasiru Ahmad El-Rufa\’i,musamman idan aka yi la\’akari da yadda yake yi wa jam\’iyya zagon kasa.

  Saboda haka mu a matsayinmu na shugabannin mazabarsa mun yanke hukuncin cewa mun dakatar da shi na tsawon watanni 11 kuma daga yau mun dakatar da shi daga duk wani al\’amari na jam\’iyya,kamar yadda takardar ta bayyana.

  Imrana Abdullahi Daga Kaduna.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here