JAM IYYAR APC TA JIHAR KADUNA TA DAKATAR DA SANATA SHEHU SANI .

    0
    1866

    RABO HALADU DAGA KADUNA

    Jamiyyar APC ta jihar kaduna ta bayar da sanarwar dakatar da Dan Majilasar dattawa mai wakiltar mazabar kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Nijeriya Sanata Shehu Sani daga jamiyyar har na tsawon watani goma sha daya.
    Sanarwan hakan ta fito ne daga bakin kakakin jamiyyar Alhaji Ibrahim wusono, a wani taron manema labarai a yau talata a sakatariyyar jamiyyar.
    Idan za a iya tunawa a makon jiya ne jamiyyar ta kafa kwamitin ladaftarwa wanda ta bukaci Sanata Shehu Sani, ya gurfana a gaban kwamitin cikin mako guda a cewar, jamiyyar idan  bai gurfanaba zasu dauki mataki mai tsauri akansa wanda a yau wa adin mako guda yacika.
    Sai dai Sanata Shehu Sani yayi nasarar raba kan yan jamiyyar a jihar ta kaduna.
    Haka kuma kalaman sun sabawa kundin tsarin mulkin jamiyyar ta APC.
    Wannan rikicin daya kunnokai a jamiyyar ta APC  a Jihar ta kaduna basa rasa nassaba da yadda Sanata Shehu Sani yake caccakar gwamna Nasiru El __Rufai wanda harkokin siyasa suke hasashen cewa Sanata Shehu Sani yana sun kujerar gwamnan jihar ta kaduna a 2019, in Allah yakaimu.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here