Za A Hukunta Duk Yan Cuwa-Cuwar kudin makamai

0
1395

Daga Usman Nasidi

Gwamnatin kasar Najeriya ta ce ta samar da wani
kwamiti mai karfi na masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa, duk wanda ya aikata laifin yin sama da fadi da kudin sayen makamai bai kaucewa hukunci ba, yayin gurfanar da shi a gaban shari\’a.

Ministan shari\’a na kasar, Abubakar Malami, shi ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi ga \’yan kungiyar \’Bring Back Our Girls\’ watau BBOG masu fafutukar ganin an kwato \’yan matan Chibok wadanda suka kai mishi ziyara a ofishinsa.

A cewar ministan shari\’ar na Najeriya, alhakin tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata laifi ba alhaki ne na ma\’aikatar shari\’a ita kadai ba.

Ministan ya kuma shaida wa \’yan kungiyar ta BBOG cewa shi a ra\’ayinsa, bai yarda a yi yarjejeniya da wanda ya yi sama da fadi da kudin al\’umma ba, ya dawo da wani daga cikin abin da ya dauka a yi masa afuwa ba, yana mai tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi doka za ta yi halinta.

\’Yan kungiyar ta BBOG, ta kai ziyara ga ministan ne da wasu bukatu da suka hada da tabbatar an hukunta mutanen da suka yi sanadiyyar sace \’yan matan Chibok, saboda karkatar da kudin makaman da ya kamata a saya wa sojoji don su ba su kariya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here