Mai Yuwu Wa A Hana Sa Hijabi-Buhari

0
1478

Rabo Haladu Daga Kaduna
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
ce mai yiwuwa gwamnatinsa ta haramta
sanya hijabi idan \’yan Boko Haram suka ci
gaba da yin amfani da mata domin kai
hare-haren kunar bakin-wake a kasar.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake
amsa tambayoyi ga rukunin \’yan jaridu ta gidan
telbijin na NTA ranar Laraba da daddare.
Wani dan jarida ne dai ya tambayi shugaban
kan cewa ko idan hare-haren kunar bakin-wake
suka ci gaba za a iya haramta sanya hijabi
kamar yadda wasu kasashe suka hana sanya
nikabi ko burqa, sai Buhari ya ce \”Kwarai
hakan ka iya faruwa\”.
Hijabi dai ya kasance suturar matan aure da
\’yan mata Musulmi masu daman gaske a
Najeriya, musamman ma a arewacin kasar.
Sai dai a baya-bayan nan hare-haren kunar
bakin-wake da \’yan mata masu sanye da hijabin
ke yi sun fara sanya shakku a zukatan mutane
dangane da kimar macen da take sanye da irin
wannan tufafi.
Sauran batutuwan da shugaba Buharin ya yi
tsokaci kai yayin hirar sun hada da kisan da
aka yi wa mabiya mazhabin Shi\’a da rikicin
Biafra da rashawa da cin hanci da kuma batun
hana yin amfani da katin ATM wajen cire
kudade a kasashen waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here