Yau Wa adin Yaki Da Boko Haram Ke Cika

0
1826

Rabo Haladu Daga Kaduna A ranar Alhamis ne wa\’adin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa
sojojin kasar domin murkushe kungiyar
Boko Haram ke cika.
A watan Agusta ne dai shugaban ya ba su
umarnin kawar da \’yan Boko Haram zuwa
karshen watan Disambar da ke karewa a yau.
A hirar da shugaban ya yi da manema labarai a makon
jiya, ya ce sojojin sun ci galaba a kan \’yan
kungiyar, yana mai cewa yanzu Boko Haram ba
ta kwace garuruwa da kauyuka kamar yadda ta
saba yi a baya.
Shugaba Buhari ya kara da cewa kisan da sojoji
ke yi wa \’yan Boko Haram ya sa ba a iya kai
hare-hare sai dai su daurawa kananan yara
mata bama-bamai, sannan su tura su cikin
jama\’a domin su tayar da su.
Sai dai duk da ikirarin da sojoji da mahukuntar
Najeriya ke yi na yin gabala a kan \’yan Boko
Haram, kungiyar na ci gaba da kai hare-hare,
musamman na kunar-bakin-wake lamarin da
kan yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Ko da a karshen makon jiya, \’yan kungiyar sun
kashe mutane da dama a Borno da Adamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here