Za a gyara garuruwan da Yan Boko Haram Suka lalata

1
1863

Daga Usman Nasidi kaduna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce nan ba da dadewa ba gwamnati za ta kaddamar da kwamitin gyara kayayyakin da aka lalata, a garuruwan da \’yan kungiyar Boko Haram
suka kori jama\’a, a gabashin kasar.

Shugaban ya ce kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Janar Theophilus Danjuma mai ritaya.

Haka kuma hanshakin dan kasuwan nan da ya
fi kowa arziki a Afirka Alhaji Aliko Dangote zai zama mamba a kwamitin.

Kwamitin zai kuma yi aikin sake tsugunar da
mutanen da kungiyar ta Boko Haram ta sa su gudun hijira.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Buhari, Mallam Garba Shehu, ya fitar, ta ce kwamitin zai tafiyar da duk kan tallafin da za a samu daga cikin gida da kasashen waje.

Sanarwar ta ce kayayyakin da kwamitin zai gyara sun hada da hanyoyin mota da
makarantu da wuraren ibada da sauransu.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here