A Kano Kotu Ta Yankewa Abdul\’aziz Dauda Hukuncin Kisangani

0
1737

Rabo Haladu Daga Kaduna
Wata babbar kotun shari\’a a jihar Kano
ta yanke wa Abdulaziz
Dauda wanda aka fi sani Abdul Inyass
hukuncin kisa.
Kotun ta same shi da laifin kalaman batanci ga
Annabi Muhammadu SAW, da kuma tayar da
hankali.
A karshen watan Mayun bara ne, a wajen wani
maulidin Shehu Ibrahim Inyass a Kano, Malam
Abdul Inyass ya yi kalaman da suka tayar da
hankula har kuma aka tuhume shi da wasu
mutane tara da laifukan da suka saba wa
dokokin jihar ta Kano.
Tun a bara dai kotun ta yanke wa sauran
mutanen tara, hukuncin kisa bisa samun su da
laifukan amma sai aka jinkirta hukuncin ga
Abdul Inyass wanda shi ne babban wanda ake
tuhuma da laifukan.
An dai gudanar da shari\’ar ce a cikin sirri.
Mutanen dai suna da damar daukaka kara a
kotun gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here