An Gurfanar Da Bello Halliru Da Dansa A Gaban Kotu

0
1163

Rabo Haladu Daga Kaduna An gurfanar da tsohon shugaban jam\’iyyar
PDP, Bello Halliru da dansa Abba
Muhammad a gaban babbar kotu a Abuja,
bisa zarginsu da yin sama da fadi na
kimanin naira miliyan 300.
Ana zargin sun karbi kudin ne daga ofishin
tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara
Sambo Dasuki, cikin kudaden da Dasukin ya
shaida wa kotu cewa an ware su ne domin
sayen kayan yaki.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin
kasa zagon kasa EFCC ce take gurfanar da su a
gaban kotun tare da kamfaninsu mai suna Bam
Properties.
Rahotanni sun ce Bello Halliru ya isa kotun ne
a kan keken guragu, a dalilin bashi da
cikakkiyar lafiya.
Bayanai sun ce shi ma kakakin jam\’iyyar PDP,
Olisa Metuh ya amsa tambayoyi gaban EFCC,
bisa zarginsa da hannu a wata badakalar kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here