Rundunar Soja Ta Karyata Zargin Fade

0
1613

RUNDUNAR sojojin Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kokarin kare mutunci da martabar yan kasa da kuma diyaucin kasar baki daya.

Bayanin hakan ya biyo bayan irin yadda ake ta cece kuce a game da irin yadda lamarin garin zariya ya kasance a kwanan baya tsakanin yayan kungiyar shi\’a da kuma sojojin Najeriya a gaban cibiyar yan shi a da suke kira Husainiyya,inda rahotanni suka yi bayanin cewa yayan kungiyar sun tsare Janar Tukur Burutai,wato dai shugaban sojojin kasa na Najeriya.

\”Ba zamu taba bari wani ko wata kungiya ta kawo wargi ga tsaron Najeriya ba,saboda mu yan kasa ne kuma ita muke yi wa aiki don haka wargi babu\”.inji shugaban rundunar soja mai kula da shiyya ta daya mejo janar A Oyebade.

Mejo janar A Oyebade,ya bayyana hakanne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa da me kaduna.

A game da batun yi wa wasu yayan kungiyar fade kuwa da mata suka kokawa manema labrai cewa an yi wa wasu mata da jami\’an tsaro suka kama kuwa, Oyebade ya ce lallai wannan batu babu kanshin gaskiya a cikinsa duk da cewa ba kowace jita jita bace zai yi magana a kai.

Oyebade, ya kuma kara da cewa su a matsayinsu na sojoji kuma yan kasa masu yi wa kasa aiki a halin yanzu da akwai matan da suka kasance zawarawa sakamakon rasa mazajensu a fagen fama ko aiki da suka kai mata sama da 500 duk tare da yayansu baki daya.

Kuma ya ce jami\’an tsro ba su da wani abu a tsakaninsu da yan shi\’a ko El zakzaky saboda sun dauki kungiyar ne kamar kowace kungiyar addini ko musulunci ko kiristanci don haka ba su da wani abu a tsakaninsu da kowa sai dai dole ne su tsare mutunci da martabar kasa ba kuma za su bari wani ya yi wargi da batun tsaron kasar ba ko wanene kuma ko su nawa ne.

\”A kokarin da muke yi na gudanar fa aiki a shekarar da ta gabata sojojin Najeriya da suke aiki a karkashin rundunarsa da suka hadar da jahohi da dama sun rasa sojoji 6 wasu 10 sun samu munana raunuka kuma guda biyu sun bace bat har yanU ana nan ana nemansu,batun makamai kuma sun samu makamai da damar gaske a hannun jama\’a inda kuma suka kama mutane kusan da 300 a wurare daban daban\”.Domin Kate hakkin jama\’a da kasa baki data sun Samar da wani sashen kula da hakkin jama\’a a rundunar domin jin koke koken da za a iya kawo was rundunar soja.
Rundunar sojan ta kuma bayar da lambobi kaar haka domin run tubarsu a sashen kare hakkin dan Adam Kamar haka lambobin 090 9970 4473,080 9808 1177 da kuma 080 2317 7699.
Imrana Abdullahi Saga kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here