Rabo Haladu Daga Kaduna
Cikin sanarwan dake dauke da sa hannun sakataren
jamiyyar PDP na Kasa Farfesa Adewole
Oladipo PDP ta bukuci
hukumar EFCC ta gaggauta sako mata
kakakin ta Mr Oliseh Metuh da ake zargi
da halarta kudin haram sama da naira
miliya dubu.
Jamiyyar ta PDP
tace kame Oliseh Metuh bai zo mata da
mamaki ba idan akayi la’akari da
barazanar da aka ce yasha huskanta daga
jamniyyar APC dama gwamnatin tarayya
wadda tace ta shiga rudani kuma take
kokarin rufe bakin ‘yan adawa sai dai mataimakin kakakin jam’iyyar
Barister Abdullahi Jalo
a cewar sa
‘’PDP tasha fadin cewa tana goyon bayan
hana cin hanci a Najeriya, shin a Oliseh
Metuh gayyatar sa da aka yi abinda
yakamata kowa ya sani cewan idan an
kama mutum cewa akayi akai shi kotu
kada ya wuce awa 24.Ai babu wanda zaice
maka an same shi da laifi kotu ce take da
wannan hurumin mu jira muji kotu me
zata yi, EFCC ai ba kotu bace haka kuma
maganganun cikin gari ba kotu bane’’
Sai dai da aka tambayi Barister cewa
sakataren jamiyyar tasu yace kame Oliseh
Metu bita da kulli ne?.
Anan ko sai yace bai yiyuwa Sakatare na
magana shi ma yana Magana.