Rabo Haladu Daga Kaduna Jam\’iyyar PDP ta bukaci hukumar
EFCC ta ci gaba da kama mambobinta da
ake zargi da hannu wajen karbar kudin
sayen makamai. Mataimakin Sakataran jamiyyar PDP Barrister Abdullahi Jallo ne yabayyanawa taron manema labari haka a Abuja.
Sai dai yace zargin da ake yi wa wasu \’ya\’yan
jam\’iyyar dangane da sama da fadi da kudin ba
zai shafi martabar jam\’iyyar ba.
Mataimakin Sakataren yada labaran Jam\’iyyar,
Barrister Abdullahi Jallo ya ce, \”Wajibi ne
mutane su sani cewa gwamnatin PDP da take
mulki a wancan lokacin ta bayar da kudin
sayen makamai. Ya kamata shugaban kasa ya
tabbatar sun amayar da kudin\”.
Barrister Jallo ya kuma bukaci hukumar EFCC
ta daure duk dan jam\’iyyar PDP da kotu ta
tabbatar ya ci moriyar kudin sayen makaman.
Ya kara da cewa kashi tamanin bisa dari na
\’yan jam\’iyyar PDP mutanen kirki ne, yana mai
cewa bai kamata a dinga yi wa \’ya\’yan
jam\’iyyar kudin-goro a kan zargin sama-da-fadi
da kudaden kasa ba.
A halin da ake ciki dai hukumar yaki da cin
hanci da rashawa wato EFCC na tuhumar wasu
ya \’yan jam\’iyyar da suka hada da tsohon
shugaban PDP na kasa, Ahaji Bello Haliru da
Kakakin jam\’iyyar Olisa Metuh da tsohon
gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu
Bafarawa kan wannan badakalar.