Rabo Haladu Daga Kaduna
Tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kaduna,
Lawal Jafaru Isa ya mayar da Naira Miliyan
100 ga EFCC, da ake zargin tsohon mai bai
wa shugaban Najeriya shawara kan
harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki ya ba
shi.
Wani makusancin Jafaru Isa ya tabbatarwa da manema labarai haka a Abuja
cewa an mika kudin ne ga hukumar EFCC.
A makon jiya ne hukumar da ke yaki da masu
yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, EFCC, ta
kama Lawal Jafaru Isa.
Ana tuhumarsa da karbar wani kaso daga cikin
dala biliyan biyu na sayen makamai, zamanin
mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck
Jonathan.
Jafaru Isa shi ne mutum na farko a makusantan
Shugaba Muhammadu Buhari da hukumar EFCC
ta kama kan zargin badakalar cin hanci da
rashawa.